Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 23 Ranan Nan da Ka Bayar Ta Faɗi Lyrics
1
Ranan nan da ka bayar ta faɗi,
Kai ne ka sa duhu ya yi.
Mu rera waƙoƙi gare ka,
Yabonka kuwa zai tsarkake mu.
2
Mun gode don Ekklesiyarka,
Da himma ta ke shaidarka,
Tana kuwa kiwon dukan duniya,
Ba ta da hutu, ko kaɗan.
3
A ƙasashen duniya dayawa,
Hasken safe ‘na ƃullowa,
Addu’a ba ta fasawa,
Yabo gare ka kullayaumin.
4
Loton da mu ke barci fa,
Waɗansu su ke farkawa,
Kowane lokaci, ƴaƴanka
Yabonka su ke furtawa.
5
Mulkinka ba zai shuɗe ba
Kamar su mulkokin duniya,
Amma ya tabbata da iko,
Har kowa ya bi nufinka.
