Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 229 Yesu, Ko Tunawa Da Kai Abu Mai Daɗi Ne Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 229 Yesu, Ko Tunawa Da Kai Abu Mai Daɗi Ne Lyrics

 

Yesu, ko tunawa da kai abu mai daɗi ne,
Amma dai, daɗin ganinka, ina misalinsa?

2
Ba waƙar duniyan nan, ko ɗaya, ko zancen masana,
Da za su iya kwatanta jamalin sunanka.

3
Mai tuba duk, sai begenka da gaskiya ya ke yi.
Wanda ya nemi fuskarka, alheri nasa ne.

4
Amma fa masu samunka, ƙaunar da ka ke yi,
Ba za a ga cikarta ba, sai wurin Masu Bi.

5
Ya Yesu, kai ne murnarmu a cikin duniyan nan,
Kai za ka zama ladanmu a cikin Sama can.

Exit mobile version