Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 228 Yesu Ya Cece Ni, Za Ya Taya Ni Lyrics
1
Yesu ya cece ni, za ya taya ni.
Muddar ya riKe ni, tsoro ba na ji.
Shi amintacce ne, sai in dogara,
Duk alkawaransa za ya aikata.
2
Yesu ya same ni, huntu, ƃatacce.
Ina so in ji shi, kullum shi kaɗai.
Sa’ad da ya kira, amsa za mu yi,
Ko’ina ya nufa sai mu riƙa bi.
3
Yesu Makiyayi, shi ya ba da rai
Kada tumakinsa duk su lalace.
Ubansa mai ƙauna yana riƙonmu,
Daga hannuwansa ba mai fizgewa.
4
Yesu Makiyayi, shi ne ƙofar rai,
Masu Bi sun shiga dukansu sosai.
Sa’ad da zai komo, za ya tattara
Dukanmu gabansa, ma ga fuskarsa.