Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 226 Allah Yana Kusa, Shi Ubanmu Ne Lyrics
1
Allah yana kusa, shi Ubanmu ne.
Ni dai ina cikinsa, shi kuwa cikina.
2
Allah yana kusa, yana tsarona.
Zarmana da tashina suna wurinsa.
3
Allah yana kusa, ko da duhu ma,
Hanyata da kwanciyata, yana shiryawa.
4
Allah yana kusa, yana taimako.
Abu duk ‘na hannunsa tun dā har wa yau.
5
Sani irin naka ya fi ƙarfina.
Ƙaunarka da saninka sun fi ganewa.
