Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 225 Yesu, Kai Ni Wurinka, Kar In Ratse Hanyarka Lyrics
1
Yesu, kai ni wurinka, kar in ratse hanyarka.
Wurinka sai lafiya, ina so in zauna can.
KORUS
Yesu, Yesu, Yesu, kai ni wurinka,
Ina so in zauna can wurinka, Mai Cetona.
2
Kai Makiyayinmu ne, babu tsoro wurinka,
Jinƙanka ya rufe ni, wa zai iya zargina?
Korus
3
Yesu, kai ni lafiya, har in isa wurinka.
Za ka shafe hawaye, gunka shi ne kwanciyar rai.
Korus
