Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 223 Mai Ceto Yana Ƙaunata Lyrics
1
Mai Ceto yana ƙaunata,
Shi Makiyayina ne.
Tun Yesu yana kiwona,
Ni ba na rasa kome.
KORUS
“Ku zo gare ni, dukanku,
Ku masu nauyin kaya,
Ni ma in ba ku hutawa,”
In ji shi, Masoyina.
2
Dā ina zaman tayarwa,
Na ƙi tafarkin Yesu,
Sai ƙaunarsa ta jawa ni,
Ta sa ni cikin garke.
Korus
3
Nan gaba dai, Ubangiji
Kullum zai bi da raina
A cikin hanyar adalci
Sabili da sunansa.
Korus
4
Ko cikin kwarin mutuwa,
Ba zan ji tsoro ba fa,
Ba wanda za ya taƃa ni,
Tun Yesu yana sona.
Korus
5
Ƙaunarsa marar ƙarewa
Nan gaba za ta bi ni.
A cikin gidan Allah kuwa
Har abada zan zauna.
Korus