Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 220 Ta Wurin Ƙaunar Mai Ceto, Sai Lafiya Lyrics
1
Ta wurin ƙaunar Mai Ceto, sai lafiya.
Ƙauna ba ta sakewa kuwa, sai lafiya.
Jininsa mai tamani ne, ƙaunarsa har abada ce,
Idonsa ya tsare mu dai, sai lafiya.
2
Ko da muna shan wahala, sai lafiya.
Shi ya iya cetonmu duk, sai lafiya.
Murnarmu daga Uban ce, ladanmu daga Yesu ne,
Tsarkakewarmu ta Ruhu, sai, lafiya.
3
Bege kuwa ya haskaka mu, sai lafiya.
Bangaskiya ta ƙarfafa mu, sai lafiya.
Mun dogara kuwa ga Allah, Yesu ne ke biyan bukata,
Ko a mace ko a raye, sai lafiya.
