Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 219 Cikin Sunan Ubangiji Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 219 Cikin Sunan Ubangiji Lyrics

 

1
Cikin sunan Ubangiji,
Kullum zan yi ta aikina.
Muradina saninka ne,
Cikin duk al’amurana.

2
Tsare ni daga tarkoki,
Ɓoye rarraunar zuciyata,
Kada ta faɗa nishaɗi
Wanda ke cikin duniya.

3
Kai ne a hannun damana,
Kai idona ke dubawa,
Domin in bi umarninka
Wanda ka nufe ni da yi.

4
Ɗawainiyarka mai sauƙi ce,
Kayanka ba mai nauyi ba,
Taimake ni in jure fa,
Har ran da zan kai mulkinka.

5
Wanda ya zo, ka karƃe shi,
Domin ya dinga aikinka.
Don haka murna na ke yi,
Har ran da zan je can Sama.

Exit mobile version