Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 218 A Cikin Dukan Halin da Mu Ke, da Murna Da Wahala Lyrics
1
A cikin dukan halin da mu ke, da murna da wahala,
Yabo na Allahna zan yi, zai riƙe zuciyata.
2
Bari mu girmama ka, Allah, mu ɗaukaka sunanka.
Cikin wahala na yi kira, ka ba ni cetonka.
3
Rundunan Allah suna nan kewaye da adilai.
Wanda ya ba da gaskiya, zai cece shi sarai.
4
Bari mu gwada ƙaunarsa, gwadawa za ta nuna
Su ne masu albarka duka, masu gaskata ka.
5
Ku ji tsoronsa, tsarkaka, ba sauran tsoro kuma.
Ku mai da aikinsa fa naku, muradinku zai biya.
6
Ga Allah Uba, Allah Ɗa, Ruhu Mai Tsarki kuma,
Mu ba ka dukan ɗaukaka, ya Allah Triniti.
