Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 217 Ya Hasken Ƙauna, Ƙaunar Allahna Lyrics
1
Ya Hasken ƙauna, ƙaunar Allahna,
Ka haskaka.
Rana ta faɗi, dubu ma ya yi,
Ka haskaka.
Wahalar raina duk ta danne ni,
Amma, ya Haskena, ka bishe ni.
2
Na daɗe fa, kai na ke ta nema,
Ka haskaka.
Kai shugaba ne, Hasken gaske kuwa,
Ka haskaka.
Duk zunubaina suna ƙaruwa
Amma, Mai Ceto, zo, ka haskaka.
3
Kai shugabana ne har abada,
Ka haskaka.
Ba wanda na ke so dai kamarka,
Ka haskaka.
Sha’anin duniya ba su ja ni ba,
Na ci nasara domin giciyenka,
4
Har ran da za ka zo ka karƃe ni,
Ka haskaka.
Ko duhu ne, ko ciwo na ke ji,
Ka haskaka.
Zan kwana lafiya a hannunka
Har ma in farka cikin ƙaunarka.