Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 216 Yesu Mai Ceto, Ni Ya Ke So Lyrics
1
Yesu Mai Ceto, ni ya ke so,
Mai pansata ne mai taimako.
Ya sha azaha don laifina,
Ya ba ni rai na har abada.
KORUS
Yesu Ɗan Allah shi na ke bi
Har za ya komo ya fyauce ni.
2
Yesu Mai Ceto, ka ƴanta ni
Daga bauta ta zunubaina.
Cika zuciya da ƙaunarka,
Kada in ƙara son duniya.
Korus
3
“In za ka bi ni.” Yesu ya ce,
“Bar neman kome, sai ni kaɗai.
Wanda ya ɗauki giciyensa
Ba za ya rasa ladansa ba.”
Korus
4
Tun da na zama masoyinsa,
Ba na jin tsoron mutuwa dai.
Gama, in ji shi, zai koma can
Ya shirya wurin zamanmu duk.
Korus
