Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 214 Alherin Yesu, Ubangijina Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 214 Alherin Yesu, Ubangijina Lyrics

 

1
Alherin Yesu, Ubangijina,
Ya wuce gaban ganewa.
Gama tun muna maƙiyansa fa,
Ya mutu don mu sami rai.

KORUS
Waɗanda suka karƃi Yesu
Ya ba su iko su zama nasa.
Ƴaƴa ne idan sun ba da
Gaskiya ga sunansa.

2
Ban iya gane ko in fassara
Abin da aka aika ba,
Amma na sani cikin zuciyata
Salama tana nan zaune.
Korus

3
Ruhu Mai Tsarki yana aikinsa
A cikin masu zunubi
Domin su san bukatar zuciya,
Su karƃi Yesu Mai Ceto.
Korus

4
Ban san ran zuwan Ubangiji ba,
Amma a shirye na ke fa
In tarbe shi a cikin sarari,
Ko kuwa in bi ta mutuwa.
Korus

Exit mobile version