Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 212 Muna Tafiya Yau Cikin Hanyar Yesu Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 212 Muna Tafiya Yau Cikin Hanyar Yesu Lyrics

 

1
Muna tafiya yau cikin hanyar Yesu.
Amma ba mu kaɗai ba ne fa.
Yesu ma yana nan, yana tare da mu,
Gama shi yana ja gabanmu.

KORUS
Kai dai ka zo, ka je tare da mu,
Cikin hanyar Mai Ceto, zuwa wurin Allah

2
Cikin ƙuncinmu duk, ya kan tallafe mu,
Yana ƙarfafa zukatanmu.
Ko jaraba ta zo, zai yi hanyar tsira,
Masu Bi duk su ci nasara.
Korus

3
Da abinci mai rai cikin Maganarsa
Ya kan ciyad da kowannenmu,
Kamar maƃulƃulai na ruwa mai rai
Ruhunsa yana cikinmu duk.
Korus

4
Ya yi alkawari, za ya ji roƙonmu,
In mun yi cikin sunan Yesu.
Sai mu ƙaunace shi, mu bi dokokinsa,
Sai mu bi shi da zuci ya ɗaya.
Korus

Exit mobile version