Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 211 Ya Yesu, Ga Ni Gabanka Lyrics
1
Ya Yesu, ga ni gabanka,
Domin in koyi gaskiyarka.
Ka nuna mini cin gaba
Da ni zan yi a hanyarka.
KORUS
Ya Yesu, buɗe idona,
Domin in gane hanyarka,
Ka nuna mini nufinka,
Ya Mai Ceto.
2
Ya Yesu, buɗe kunnena,
Domin in ji maganarka.
Ni ina so in bi nufinka,
In yi abin da ka ke so.
KORUS
Ya Yesu, buɗe kunnena,
Domin in ji maganarka,
Ka nuna mini nufinka,
Ya Mai Ceto.
3
Ya Yesu, buɗe bakina,
Domin in shaida ko’ina
Ceton da ka yi wa duniya
Da gafarar zunubanmu.
KORUS
Ya Yesu, buɗe bakina,
Domin in shaida cetonka,
Ka nuna mini nufinka,
Ya Mai Ceto.
4
Yesu, juyad da zuciyata,
Domin in nuna halinka
Ƴanuwana su dube ni,
Har su ga Allah cikina.
KORUS
Yesu, juyad da zuciyata
Domin in nuna halinka,
Ka nuna mini nufinka,
Ya Mai Ceto.
5
Ya Yesu, ba ni zarafi
Domin in yi ta aikinka,
Ƴanuwana su rinjayu
Su ma su shiga hanyarka.
KORUS
Ya Yesu, ba ni zarafi
Domin in yi ta aikinka,
Ka nuna mini nufinka,
Ya Mai Ceto.