Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 21 Yinin Nan Ya Wuce, Dare Yana Bi Lyrics
1
Yinin nan ya wuce, dare yana bi,
Babu sauran haske, duhu yana yi.
2
Su taurari duka, aikin hannunka,
Su rundunan sama, suna walƙiya.
3
Yesu, Mai Alheri, sa albarkarka,
Bisa ƙanƙanana, yaran ƙaunarka.
4
Tsare mu da dare, inuwantad da mu,
Ta dalilin barci, ba mu ƙarfinka.
5
Yafe zunubanmu, wanke zukata,
Ba mu naka iko, gyarta ha1inmu.
6
Daga tarkon Iblis, daga wayonsa,
Algus, duk da ƙarya, ceci ƴaƴanka.
7
Duba masu ciwo, rage zafinsu,
Lura da marayu, ji addu’arsu.