Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 208 Yabi Yesu, Ku Bayinsa Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 208 Yabi Yesu, Ku Bayinsa Lyrics

 

1
Yabi Yesu, ku bayinsa,
Zo, ku ɗaukaka sunansa,
Sai da murna za mu gusa
Wurinsa yanzu.

2
Sunan Yesu ya tsare mu,
Hannunsa ya tokare mu,
Ko menene ya same mu,
Mu ne ƴaƴansa.

3
Kafa begenku gare shi!
Ba zai sāke ba, in ji shi.
Daga ayyukan maƙiyi
Za ya cece ku.

Exit mobile version