Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 206 Lokacin da Ka Ke Shan Wahala Fa Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 206 Lokacin da Ka Ke Shan Wahala Fa Lyrics

 

1
Lokacin da ka ke shan wahala fa,
Lokacin da Shaiɗan ya ke damunka,
Tuna da alherin Ubangiji inka,
Wannan dai zai ba ka karfin zuciya.

KORUS
Har matuka Yesu yana nan
Har matuka Yesu yana nan
Har matuka Yesu yana nan
Shi ba zai rabu da kai ba, ko kaɗan.

2
Sa’ad da ka duba masu dukiya,
Tuna da alkawarin Mai Cetonka,
Rai madauwami ne shi ya ce zai bayar
Ga duk wanda ya ke ba da gaskiya.
Korus

3
Idan ka gaji da halin duniya,
Kana neman rabuwa da ruɗinta,
In ji Ubangiji, “Ina jiranka,
Zo, ka karƃi hutawa a wurina.”
Korus

4
Ko a matse ka ke, babu fasawa,
Shaiɗan yana neman ƃata halinka,
Sai ka ta da murya ga Allahnmu,
Shi ba za ya yarda ba ka lalace .
Korus

Exit mobile version