Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 205 Ka Bi da Ni, Ya Ubangijina Lyrics
1
Ka bi da ni, ya Ubangijina,
A duniyan nan,
Na ƃata dai, ban san hanyarka ba,
Ka bi da ni.
Tsare zamana, tsare tashina,
Inda na je, ka riƙe hannuna.
2
Da idonka, ya Ubangijina,
Ka bi da. ni,
Hasken mutane, hasken duniyan nan,
Ka bi da ni.
In ban da kai, tuntuƃe na ke yi,
Ya kai Shugabana, ka bi da ni.
3
Ruhu Mai Tsarki, Ruhun taimako
Zai bi da ni.
Ko cikin lafiya ko cikin cuta,
Zai bi da ni.
Shi ma zai zama Jagabana kuwa
Har ranar da zai cika cetona.