Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 200 Ruhu Na Alheri, Zo, Ni da Kaina Ina So Lyrics
1
Ruhu na alheri, zo, ni da kaina ina so.
Zauna cikin zuciyata don in zama kamarka,
Ba ni halin taimako duk da na tawali’u.
2
Ruhun gaskiya, ka zo, ni da kaina ina so.
Gaskiya ta kasance, har ta bi da ni sosai.
Cikin dukan aikina, kau da halin ƙarya.
3
Ruhun Allah, sai ka zo, ni da kaina ina so.
Raba ni da zunubi, don in aika adalci.
Dukan nawa sai in ba Yesu Ubangijina.