Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 20 Yesu Ubangijinmu, Ga Mu Nan A Gabanka Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 20 Yesu Ubangijinmu, Ga Mu Nan A Gabanka Lyrics

 

1
Yesu Ubangijinmu, ga mu nan a gabanka.
Kai ka kawo dukanmu yinin nan da lafiya
Muna rera waƙarmu, muna maka godiya.

2
In yau wata jaraba za ta kai mu haɗari,
Ba mu ikon jurewa, ƙara mana ƙarfi kuwa,
Kiyaye mu lafiya, har mu ka da zunubi.

3
Bisa ga maganarka, daidaita rayukanmu,
Bishe mu da Ruhunka, amshi mulkin nufinmu.
Bar mu miƙa gare ka hadaya ta zuciyarmu.

4
Ji yanzu addu’armu, ji mu, muna roƙonka.
Da mu duk da ƴanuwa, baiwarka mafificiya
Ita ce bukatarmu, sahihiyar zuciya.

5
Haka za mu bayyana yau da gobe godiyarmu.
Haka za mu ɗaukaka sunan Ubangijinmu.
Za mu shaida yabonka, Almasihu Allahnmu.

Exit mobile version