Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 2 Ubanginmu, Mai Ceto Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 2 Ubanginmu, Mai Ceto Lyrics

 

1
Ubanginmu, Mai Ceto,
Don zumunta ne muka zo.
A duniyan nan sai sakewa,
Wurinka fa sai hutawa.

2
Tun jiya, yau, har abada,
Madauwami ne sunanka!
Kai ne ka kafa duniyan nan,
Kai ne mai shirya gida can.

3
Almasihu, Cetonmu,
Ba mu da wani taimako,
Amma ƙaunarka cikakkiya,
Ita ce garkuwar ƴaƴanka.

4
Ƙaunarka ! har wa yau ta tsaya
Da, ka ɗanɗana mutuwa.
Can bisa kursiyin Allahnmu,
Yanzu ka rayu dominmu.

5
Yabo, daraja, godiya
Gare ka Yesu Ɗan Allah!
Ka cika mu da Ruhunka,
Ya koya mana nufinka.

Exit mobile version