Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 199 Ya Ruhun Allah, Zo Yanzu Lyrics
1
Ya Ruhun Allah, zo yanzu
Ka sauko nan, ka cika mu.
Ruhu mai shafewa ne kai,
Mai ba da kyautar sabon rai.
Sai dai ka ba mu kyautarka
Da hasken rai da ƙaunarka.
2
Kullum ka ba mu haskenka
Domin mu bi ka, Shugaba.
Ka cika mu da murnarka,
Ka haskaka fuskokinmu,
Jaraba duk, ka kore ta,
Inda ka ke, sai lafiya.
3
Kai Kyautar Allah, Ruhunsa,
Mai koya mana sanin Ɗan,
Ka nuna mana ƙaunarsa
Domin mu riƙa yabonsa.
Mu yi yabo ga Allahnmu
Mai ba da haske da ƙauna.
