Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 197 Ya Ruhun Allah, Ruhun Rai, Ka Ji Addu’armu Lyrics
1
Ya Ruhun Allah, Ruhun rai, ka ji addu’armu,
Ka sauko nan da ikonka, Ruhu mai taimako.
2
Ya Ruhun haske, ga mu nan, mun kira ka yanzu,
Ka haskaka zukatanmu, ka kori duhunsu.
3
Ya Ruhun wuta, tsarkake harsunan bayinka,
Har za mu ba da shaidarka da ƙarfin zuciya.
4
Ya Ruhun ƙauna, cika mu da ƙauna cikakkiya,
Domin mu zama kamarka tun yau har abada.