Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 196 Ya Yesu, Ruhunka Kaɗai Zai Juye Zuciyarmu Lyrics
1
Ya Yesu, Ruhunka kaɗai zai juye zuciyarmu,
Ikonsa ma a cikinmu zai sake halinmu.
KORUS
Ya Ruhu mai taimako, wurinmu duk ka zo,
Ka cika dukan zuciyarmu, ka ba mu ikonka yau.
2
Ya Yesu, Ruhunka kaɗai, zai ba mu ƙaunarka,
Ikonsa cikin ranmu kuwa zai juye gurinmu.
Korus
3
Ruhunka, Yesu, ƙauna ne, Ruhun bangaskiya kuwa.
Shi fid da kwaɗayinmu duk da ikon ƙaunarsa.
Korus
4
Ya Ruhun Yesu, muna so ka ji addu’armu,
Ka sauko nan da ikonka, ka zauna bisanmu.
Korus