Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 195 Mai Fansarmu, da Za Ya Hau Ya Bar Mai Taimako Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 195 Mai Fansarmu, da Za Ya Hau Ya Bar Mai Taimako Lyrics

 

1
Mai fansarmu, da za ya hau ya bar mai taimako
Ya bi da mu, ya zauna kuwa a cikinmu.

2
Shugabanmu, mai bayarwa, da yardar rai ya zo,
Ya hura mana ƙaunarsa a zuciyarmu.

3
Ya. zo da kamar kurciya, shaidar salama shi,
Da nufin ba da lafiya ga duniya duko

4
Tasa kuwa wannan murya a zuciya mu kan ji,
Mai tsautawa, mai ta’aziyya, mai ƙauna kuwa.

5
Idan fa mun yi nasara, idan da tsabtar rai,
Ko tunani mai tsarki, shi ne ya bayar.

6
Ya Ruhun Tsarki, Ruhun Rai, bayyana ikonka,
Ka kau da rashin ƙarfinmu, ka cika mu.

Exit mobile version