Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 194 Ka Zo da Ruhunka, Ya Allah, Bisanmu Lyrics
1
Ka zo da Ruhunka, ya Allah, bisanmu,
Domin mu nemi nufinka, mu danne gurinmu.
2
Ka zo da Ruhunka, ya Allah, bisanmu,
Domin a wanke zuciyarmu, a gyara halinmu.
3
Ka zo da Ruhunka, ya Allah, bisanmu,
Don tsarkinka da ikonka, su zauna a cikinmu.
4
Ka zo da Ruhunka, ya Allah, bisanmu,
Domin mu zama shaidunka, mu juyo da danginmu.