Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 193 Kamar Ruwa Ya Kan Sauko Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 193 Kamar Ruwa Ya Kan Sauko Lyrics

 

1
Kamar ruwa ya kan sauko
Bisa duniya busasshiya,
Haka Ruhun Ubangiji
Cikin can Ekklesiya,
Sauko nan, ya Ruhun Allah,
Sauko, muna kishinka. (2x

2
Kamar raƃa ta kan faɗo
Bisa ƙasa, ta kan tsaya,
Ba ta fita, sai ta gama
Nata aikin warkarwa.
Sauko nan, ya Ruhun Allah,
Sauko, muna jiranka. (2x

3
Kamar wuta ta kan cinye
Dauɗa, cuta, ruƃewa,
Haka Ruhun Ubangiji,
Zauna cikin zuciya.
Kau da ƙarya, dukan lafi,
Kone su da wutarka. (2x

4
Aikin Ruhu mu ke roƙo,
Ƴaƴansa na lafiya.
Ƙaunar Ruhu mu ke nema,
Ƙauna marar ƙarewa,
Ba mu su, ya Ruhun Allah,
Ba mu su, ba fasawa. (2x

Exit mobile version