Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 192 Ya Yesunmu, Mun Taru Wurinka Lyrics
1
Ya Yesunmu, mun taru wurinka.
Ka ji roƙonmu, mu ne ƴaƴanka.
Ya Ruhun Allah, buɗe zuciyarmu,
Yi aikinka, ya Ruhu, cikinmu.
2
Bayyana kanka cikin ƙaunarka.
Bishe mu kuwa ta wurin Ruhunka.
Mai Taimako fa cikin zuciya,
Zai buɗe mana dukan gaskiya.
3
Ruhunka Yesu, Ruhunka kaɗai
Zai tsarkake zukatanmu sarai.
Ikonsa ne zai juye nufinmu,
I, daga ƙeta zuwa Allahnmu.
4
Ruhun bangaskiya, Ruhun ƙauna kuwa,
Ruhu Mai Tsarki, kyautar hannunka,
Shi zo, shi sauko bisa dukanmu,
Ikonsa kuwa shi zauna cikinmu.