Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 191 Dā, Na Zauna Cikin Zunubi Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 191 Dā, Na Zauna Cikin Zunubi Lyrics

 

1
Dā, na zauna cikin zunubi,
Ba na kula da Ubangiji,
Ko mutuwa wadda shi ya yi
Kan giciye.

KORUS
Jinƙan Yesu, ba misalinsa,
Ya yi mini aikin gafara.
Kayan laifina ya ɗauka kuwa
Kan giciye.

2
Na ji zancen ladan zunubi.
Tsoron mutuwa ya kama ni.
Sai na roƙi jinƙan Mai Ceto
Kan giciye.
Korus

3
Na yi murna marar iyaka
Tun da Yesu ya yi cetona.
Ina rera waƙar yabonsa,
Ba fasawa.

4
Nufina in kawo daraja
Wurin Yesu Ubangijina,
Sa’an nan in dubi fuskarsa
Har abada.

Exit mobile version