Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 190 Yesu Ya Zo Da Ƙaunarsa Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 190 Yesu Ya Zo Da Ƙaunarsa Lyrics

 

1
Yesu ya zo da ƙaunarsa,
Ya fanshe ni da jininsa,
Ya cece ni da ikonsa,
Yana riƙe da ni.

KORUS
Yesu ya ba da jininsa,
Ya wanke dukan laifina,
Ya kawo mini gafara.
Ina yabon Yesu yanzu.

2
Tun da ya kira ni, na ƙi,
Amma yanzu, Yesu zan bi,
Ina misalin kyautarsa
Da daɗin bautarsa!
Korus

3
Yesu ya kawo gafara,
Ya cika ni da Ruhunsa,
Ya sake mini halina,
Ubangijina ne.
Korus

Exit mobile version