Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 189 Dā, Ban San Labarin Yesu Ba Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 189 Dā, Ban San Labarin Yesu Ba Lyrics

 

1
Dā, ban san labarin Yesu ba,
Cikin duhu na bi hanyata,
Ban ko kula akwai ceto ba
Gun giciye.

KORUS
Jinƙai marar iyaka ne fa.
Gafara a yalwace ya yi,
Har ya kau da dukan zunubi
Kan giciye.

2
Da na ji labarin cetonsa,
Na ji nauyin kayan laifina.
Sai na tashi neman gafara
Gun giciye.
Korus

3
Duba yawan girman ƙaunarsa,
Duba irin aikin gafara!
Da jininsa ne ya fanshe mu
Kan giciye.
Korus

4
Daga nan na zama bawansa,
Ya yarda ya zama Sarkina.
Akwai murna cikin zuciyata
Don giciye.
Korus

Exit mobile version