Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 184 Ya Yesu, Kayan Adona Jininka Ne Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 184 Ya Yesu, Kayan Adona Jininka Ne Lyrics

 

1
Ya Yesu, kayan adona
Jininka ne da giciyenka.
Ko duniya dai ta yi gobara,
Yafe da waɗannan zan tsaya.

KORUS
Kan Yesu, Fan Ceto, na tsaya,
Ba wani wurin rai, ko ɗaya.
Ba wani wurin rai, ko ɗaya.

2
Ko zunubaina sun yi yawa
Har ba mai iya ƙirgawa,
Ba wanda ba a shafe ba
Ran da ka ba da jininka.
Korus

3
Dabarun duniya suna nan,
Dabarun banza na Shaiɗan.
Tawa dabara ɗaya ce,
Cetona jinin Yesu ne.
Korus

4
Domin shari’ar Lahira,
Yesu, na fake wurinka.
Ban duba nawa aiki ba,
Gare ka ne na dogara.
Korus

5
A ƙofar Sama, izinina
Sai jininka da giciyenka.
Ko gaban kursiyi, murnata
Jinin Yesu da ƙaunarsa.
Korus

Exit mobile version