Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 183 Cikin Yesu Almasihu Zan Dogara Lyrics
1
Cikin Yesu Almasihu zan dogara.
Aikin ceto duk ya cika, zan dogara,
Ba a cikin aiki nawa,
Ko a cikin nagartata,
Sai dai cikin aikin Yesu zan dogara.
2
Cikin giciyen Almasihu, ga gafara.
Ko mutane ba sa yarda, ga gafara.
Fansarmu wurinsa ta ke,
Almasihu Mai Cetonmu,
Giciyen ya kai mu gunsa, ga gafara.
3
Jinin Ubangiji Yesu ya wanke ni.
Jininsa mai daraja ne, ya wanke ni.
Laifina mai dauɗa baki,
Jininsa ya tsarkake ni.
Cikin jininka, ya Yesu, ka wanke ni.
4
Cikin ƙaunar Almasihu, ga hutawa.
Ta fi ƙaunar iyayenmu, ga hutawa.
Ƙaunarsa fa ba kamarta.
Ko zunubi, ko jaraba,
Yesu ne zai ci nasara, ga hutawa.
5
Zuwan Yesu Almasihu na gaskata.
Bisa ga alkawarinsa, shi ne zai dawo.
Zo da sauri, Ubangiji,
Sake halina da jiki,
Taka ce sarautar kome har abada.
