Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 181 A Cikin Zuciyata Na Ji Muryar Mai Cetona Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 181 A Cikin Zuciyata Na Ji Muryar Mai Cetona Lyrics

 

1
A cikin zuciyata na ji muryar Mai Cetona.
“Ka zo gare ni nan”, ta ce, “In ba ka hutawa”.
Na zo gun Yesu hakanan, da zunubi mai yawa,
Ya saukar mini fa da su, ya ba ni warkarwa.

2
Muryar ta kuma ce da ni, “Ga ruwan rai na bayar.
Ka zo, ka sunkuya, ka sha, ka daina ƙishirwa.”
Na zo gun Yesu fa, na sha daga rijiyar rai.
Kishi ya ƙare, na natsu, raina ya wartsake.

3
Muryar Mai Cetona ta ce, “Ni hasken duniya ne.
Wanda ya zo gun haskena, ransa zai tsarkake.”
Na zo na shiga haskensa, ya rayad da ruhuna,
Har abada kuwa nan na ke gun Yesu, Sarkina.

Exit mobile version