Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 180 A Cikin Yesu Na Sami Rai, A Cikinsa Kaɗai Lyrics
1
A cikin Yesu na sami rai, a cikinsa kaɗai,
Salama kuwa da kwanciyar rai, murna ba fasawa.
KORUS
Yesu shi ne Mai Cetona, ba wani wanda na fi so.
Salama, murna, kwanciyar rai, sai cikin Almasihu.
2
Raina bai sami hutu ba a cikin duniyan nan,
Amma ƙaunar Mai Cetona ta hutasshe ni nandanan.
Korus
3
Dā mutane suka kashe shi, amma ya tashi kuwa.
Shi kuma za ya dawo nan, zai karƃi mulkinsa.
Korus
4
Mai zuwa ba ya korarsa, mai tuba kuwa ba ya ƙi.
Kuma mai ba da gaskiya, Yesu zai cece shi.
Korus