Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 179 Na Ji Kiranka, Ya Mai Cetona Lyrics
1
Na ji kiranka, ya Mai Cetona,
Na ji zancen ƙaunarka,
Da gafararka daga zunubi
Da ka yi dominmu duk.
KORUS
I, zan bi ka, ya Mai Cetona,
Zan dai kama hanyarka,
Yau na zo wurinka domin gafara,
Sai ka ji roƙona yau.
2
Na gaji da bin hanyoyin Shaiɗan
Na gaji da bautarsa,
Ba ya kyauta wa masu binsa fa,
Mutuwa ce ladansa.
Korus
3
Ina neman murna da kwanciyar rai,
Ina neman gafara,
Ban same su ba cikin duniya
Sai a wurinka kaɗai.
Korus
4
Duk wahalar duniya da zafinta
Wanda Masu Bi ke ji,
Ba ya kai ga bege na daraja
Wanda ya ke cikinka.
Korus
