Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 178 Yesu Mai Jin Tausayi, Ga Ni Nan A Gabanka Lyrics
1
Yesu mai jin tausayi, ga ni nan a gabanka.
Ni na cika zunubi, laifina ya kā da ni.
Babu wani Mai Ceto sai dai kai. ya Almasihu.
2
Kome niyyar da na yi garin zaman adali,
Ko ƙoƙari na ke yi garin barin zunubi
Duk ya kasa cetona, sai ka sake halina.
3
Ban da kuɗin fansata, ga ni nan a wurinka.
Sai ka kau da laifina da jininka, Ɗan Allah.
Sai ka ba ni sabon rai har in bi ka, kai kaɗai.
4
Cikin duniyan nan yanzu haɗa ni da cetattu.
Kome wuya, sai in bi kusa da Ubangiji,
Ba da ikon kaina ba, sai da ikon Ruhunka.