Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 176 Na Ta da Idona Wurin Mai Cetona Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 176 Na Ta da Idona Wurin Mai Cetona Lyrics

 

1
Na ta da idona wurin Mai Cetona,
Wurin Yesu.
Na bata hanya fa, na faɗa jaraba,
Sai ka ji roƙona, Mai Cetona.

2
Na faɗi laifina, na faɗi aibina
Wurin Yesu.
Zuciyata mai dauɗa, ka iya wankewa.
Sai ka ji roƙona, Mai Gafara.

3
Shugabance ni dai a wannan duniya,
Ina addu’a.
Kwaɗayin zuciyata ya kawo jaraba.
Ka iya gyartawa, Mai Cetona.

4
A ranar mutuwa, sai ka bishe ni kuwa
Har Sama can.
Saboda giciyenka, ina da fansata,
Nan gaba na yarda in bi Yesu.

Exit mobile version