Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 170 Yesu, Dutsen Cetona, Bar In Ɓuya Wurinka Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 170 Yesu, Dutsen Cetona, Bar In Ɓuya Wurinka Lyrics

 

1
Yesu, Dutsen Cetona, bar in ƃuya wurinka.
Jini, fansar mutane; ruwa, tsarkakewar rai,
Ga su, suna zubowa daga cikin zuciyarka.

2
Hannu wofi fa na zo, jinƙanka ne na ke so.
Dukan zuciya, dukan rai, duk ƙazanta ne kaɗai.
Ga ni wurin giciyenka, ina neman gafara.

3
Kome yawan aikina, bai isa cetona ba.
Ko ban huta ba daɗai, kullum ina hawaye,
Dukan wannan banza ne, kai kaɗai Mai Ceto ne.

4
Ran da za a binne ni, ko kuwa za a fyauce ni,
Ran da zan bar duniyan nan, Zan dai gan ka zaune can,
Amma kamin ranan nan, bar in ƃuya wurinka.

Exit mobile version