Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 169 Ya Yesu Ubangijina Ba Kome Cikin Hannuna Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 169 Ya Yesu Ubangijina Ba Kome Cikin Hannuna Lyrics

 

1
Ya Yesu Ubangijina
Ba kome cikin hannuna,
Ba hujja domin laifina,
Mai biyan fansa, na zo, na zo.

2
Alkawarinka na ke bi.
Ba ka korar mai zunubi,
Mai tuba za ka karƃe shi,
Mai biyan fansa, na zo, na zo.

3
Dube ni marar ƙarfi fa.
Ka biya bukatar ruhuna.
Addu’ar kowa ba ka ƙi,
Mai biyan fansa na zo, na zo.

4
Ba ni da kome ban da kai,
Ko kyau ko gaskiya ko rai,
Kai ne Mai Ceto, kai kaɗai,
Mai biyan fansa, na zo, na zo.

5
Ƙaunarka marar iyaka,
Ta sa ni cikin hanyarka,
Ni bawanka har abada,
Mai biyan fansa, na zo, na zo.

Exit mobile version