Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 168 Ya Almasihu, Ga Ni Nan Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 168 Ya Almasihu, Ga Ni Nan Lyrics

 

1
Ya Almasihu, ga ni nan,
Na zo gare ka ƃatacce.
Ba wanda za ya cece ni,
Ba taimako, sai kai kaɗai.

KORUS
Ga ni nan, ga ni nan,
Ya Almasihu, ga ni nan.
Na zo da kayan zunubi,
Ka kau da shi, ka wanke ni.
Ga ni nan, ga ni nan,
Ya Almasihu, ga ni nan.

2
Ban zo da kuɗin fansa ba,
Ba kome nan sai zunubi,
Amma na duba jininka,
Ka ji tausayi, ka karƃe ni.
Korus

3
An gama aikin cetona,
Ga jininka ya fanshe ni.
Yanzu na zama bawanka,
Har abada ni naka ne.
Korus

Exit mobile version