Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 167 Ya Allah Uba, Ga Ni Nan Lyrics
1
Ya Allah Uba, ga ni nan,
Ba kai ne ka kira ni ba?
Mai yalwar jinƙai, yafe ni,
Na zo, na zo, ka cece ni.
2
Ya Yesu, kai mai iko ne,
Alheri, ceto naka ne.
Sai ka ji kukana yanzu,
Na zo, na zo, Mai Cetona.
3
Ya Ruhun gaskiya, Ruhun rai,
Ni ne na bata zuciyarka.
A cikin rashin ƙarfina
Na zo, na zo, ka cika ni.
4
Ubangiji, Almasihu,
Ƙaunarka ce ta jawo ni,
Ba za ka ƙi mai sonka ba,
Na zo, na zo, ka karƃe ni.
