Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 163 Babban Mai Magani ‘Na Nan Lyrics
1
Babban mai magani ‘na nan,
Yesu mai jin tausayinmu.
Mu je mu nemi warkewa
A wurin Almasihu.
KORUS
Yesu! suna mai daɗin ji,
Ba mai kamarsa, ba mai fi.
Ina sonsa kamar me !
Yesu Almasihu.
2
Mai ba da lafiya ne shi,
Cuta fa zunubanmu.
Mu je mu roƙi gafara
A wurin Almasihu.
Korus
3
Mai kawo gafara ne shi,
Ya ɗauke zunubanmu,
Ya kai su bisa itacen
A cikin jiki nasa.
Korus
4
Nan gaba za mu yabe shi,
Mun komo lafiyayyu.
Ba magani na zunubi
Sai wurin Almasihu.
Korus
5
Amma da dangi masu yawa
Da ba su da cetonsa,
Mu sai mu je mu neme su,
Mu kai su wurin Yesu.
Korus