Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 162 Zo, Kowane Mai Zunubi, Ka Nemi Gafara Lyrics
1
Zo, kowane mai zunubi, ka nemi gafara.
Yesu ya yi alkawari zai ba ka nasara.
KORUS
Gaskata shi, gaskata shi, gaskata shi yau
Zai karƃe ka, zai karƃe ka, zai karƃe ka yau.
2
Yesu ya ba da jininsa, jini mai daraja
Har ma ya sha hukuncinka domin ka barata.
Korus
3
Yesu shi ne mai ba da rai, shi ne mai gaskiya,
Ka dogara gare shi dai, zai tsare zuciyarka.
Korus