Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 161 Babban Malami Ne Ya Zo da Dare Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 161 Babban Malami Ne Ya Zo da Dare Lyrics

 

1
Babban malami ne ya zo da dare
A wurin Yesu don ya tambaye shi
Zancen hanyar ceto, har Yesu ya ce,
“A haife ka kuma.”

KORUS
Dole a haife ka, a sake haihuwarka,
Hakika, mai neman shiga Sama can
Dole haihuwa sau biyu.

2
Ku mutane duk, kasa kunne a nan
Ga zancen Yesu Ubangijinmu dai,
A bin da ya ce ya shafe mu duka,
“A haife ku kuma.”
Korus

3
Idan kana so ka kai wurin Allah,
Ka huta a cikin gidan daraja,
Idan kana son rai na har abada,
A haife ka kuma.
Korus

4
“Zancen nan da wuya, ba dama.” ka ce
Ka zo wurin Yesu, zai yiwu sosai
Shi yana da ikon al’ajabi fa,
Zai sake haihuwarka.
Korus

Exit mobile version