Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 160 Yesu, Mai Ceto, ‘na Kiranku Yau Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 160 Yesu, Mai Ceto, ‘na Kiranku Yau Lyrics

 

1
Yesu, Mai Ceto, ‘na kiranku yau,
Ko kuna ji, ko ba ku ji.
Gara ku kasa mar kunne da kyau,
Sanadin ceto ne shi.

KORUS
Ko kuna ji, ko ba ku ji,
Yesu Mai Cetonku
Kiranku yau ya ke yi.

2
Ba inda ba shi, shi mai kiran nan,
Ba shakka dai, gaskiya ne.
Kusa da kowa, shi Mai Taimakon,
Ga shi kurkusa da ku.
Korus

3
Yaya sunansa, shi mai kiran nan?
Shi Yesu ne, shi Aikakke,
Kristi, Dan Allah ma, Maɗaukaki,
Babu kama tasa dai.
Korus

Exit mobile version