Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 16 Ni Na Gaskata da Allah Lyrics
1
Ni na gaskata da Allah,
Ga shi, uku cikin ɗaya,
Uba, Ɗa da Ruhu kuma.
Allahntakarsu ɗaya.
2
Allah mai yin haskoki ne,
Shi Mahaliccinmu ne,
Har da duniya, duk da Sama,
Taurari da masu rai.
3
Allab Ɗa shi ya fanshe mu,
Shafaffe da Aikakke
Daga wurin Allah Uba,
Shi ne Hanya, Gaskiya, Rai.
4
Allah Ruhu Mai Tsarki kuwa,
Ba wurin da babu shi,
Ikon Allah a gare shi,
Shi Mai Tsarkakewa ne.
5
Allahntaka ga Triniti,
Ɗaya ne, ba uku ba,
Allahnmu Madauwami kuwa,
Gabansa mu rusuna.