Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 159 Alherin Ceto, Ga Shi Nan Lyrics
1
Alherin ceto, ga shi nan,
An shirya shi dayawa fa
A wurin Yesu, Aikakken.
Mai nema ba zai rasa ba.
2
Da ya ke yana kusa dai,
Shi kuma yana samuwa,
Ka jingina gare shi fa,
Duk kwananka a duniya.
3
Duk shakkarsa ka daina yi,
Ɗan Allah ku ka ƙaryata.
Tun faɗa tasa tana nan,
Alkawarin, ka gaskata.