Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 158 Sai Wata Rana,In Ji Mutum Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 158 Sai Wata Rana,In Ji Mutum Lyrics

 

1
“Sai wata rana,” in ji mutum,
“Sai wata rana, ni ma zan bi,
Ba dama tukuna, yanzu ba zarafi,
Sai wata rana dai, zan bi Yesu.”

2
“Zo, zo, yanzu dai,” in ji Yesu,
“Kada ka daɗe, ka lalace.
Ina ta kiranka, zo, zo a wurina,
Ni ne Mai Cetonka, Masoyinka.”

3
“Sai wata rana,” in ji Shaiɗan,
Sai wata tana, sai halaka.
Dama ‘na wucewa, ƙofa ‘na rufewa,
Saura kaɗan, ayya-Gidan Wuta !

Exit mobile version