Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 156 Zo Gare Ni, Masu Kaya Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 156 Zo Gare Ni, Masu Kaya Lyrics

 

1
Zo gare ni, masu kaya,
Masu shan wahala ma,
In ji Yesu Mai Cetonmu,
Ni in ba ku hutawa.

KORUS
Akwai hutu kuwa mai daɗi,
Wurin Ubangijinmu.
Sai ku tashi, zo wurinsa,
Zai saukad da kayanku.

2
Kayana fa marar nauyi,
Karkiyata mai sauki ce.
Sai ku koya a wurina,
Za ku sami hutawa.
Korus

3
Ga shi, kayanku da nauyi,
Kuna shan wahala kuwa,
In kun dogara ga Yesu,
Shi zai ɗauke kayanku.
Korus

Exit mobile version